’Yan sanda sun kwato wayoyi 41 da ƙwayoyi da ake zargin sun kai Naira miliyan 6.5 a Borno
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta ce ta kwato wayoyin hannu 41 tare da wasu ƙwayoyin da ake zargin haramtattu ne, waɗanda darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 6.5.
Rundunar ta ce an samu kayayyakin ne a yayin wasu ayyukan sintiri da samamen da jami’anta suka gudanar domin yaƙi da aikata laifuka a jihar.
’Yan sandan sun ce suna ci gaba da bincike kan waɗanda aka kama da kuma inda kayayyakin suka fito, kafin a ɗauki matakin doka a kansu.