Diphtheria: Adadin Waɗanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 27 A Plateau

0 47

Diphtheria: Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 27 a Plateau

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon barkewar cutar diphtheria a Jihar Plateau ya kai 27, yayin da hukumomin lafiya ke ci gaba da ɗaukar matakan dakile yaɗuwar cutar.

Diphtheria cuta ce mai yaɗuwa wadda ke iya shafar makogwaro da hanyoyin numfashi, kuma yara na daga cikin waɗanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da ita. Rigakafi na daga cikin muhimman hanyoyin kariya daga cutar.

Leave a Reply