An Kama Mutane Biyu A Kano da Suka Shirya Yin Garkuwa da Wani Dagaci

0 9

Jami’an ƴan sanda sun kama wasu matasa biyu a Jihar Kano bisa zarginsu da shirya garkuwa da shugaban ƙauyen Bangare da ke Karamar Hukumar Gezawa ta jihar.

An kama waɗanda ake zargin, Aliyu Naziru Garba, mai shekara 20, da Bashir Alhasan, mai shekara 20, bayan wani samame na musamman da jami’an tsaro suka gudanar sakamakon bayanan sirri da suka samu bayan da Dagacin ƙauyen, Mallam Idris, ya karɓi barazana ta wayar tarho.

A cikin wata sanarwa da ya fitar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa Dagacin ƙauyen ya kai rahoton lamarin ofishin rundunar ‘ƴan sanda ba Gezawa a ranar 26 ga Oktoba.

A cewar sanarwar, wanda ya kira wayar ya yi barazanar yin garkuwa da Dagacin ƙauyen da misalin ƙarfe 9:33 na dare, lamarin da ya sa jami’an ‘yan sanda suka fara bincike, wanda daga bisani ya kai ga cafke waɗannan mutum biyu.

‘Yan sanda sun ce waɗanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi yayin bincike, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner