Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da ke ƙalubalantar damar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin ranar Talata, inda ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar na da cikakkiyar damar sake neman takara a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kotun ta kuma ci tarar wanda ya shigar da ƙarar, Johnmary Jideobi, kuɗi har naira miliyan 21, ciki har da naira miliyan 20 da za a bai wa Jonathan, sai kuma naira miliyan ɗaya da za a bai wa Babban Lauyan Tarayya.
Alƙalin ya bayyana cewa mai ƙarar ba shi da hurumin shigar da ƙarar, domin bai nuna wata illa kai tsaye da zai fuskanta ba dangane da yiwuwar Jonathan ya tsaya takara a 2027.
Mai shari’ar ya ce tuni kotuna a Yenagoa da Kotun Ɗaukaka Ƙara suka riga suka yanke hukunci cewa Jonathan na da damar sake neman shugabancin ƙasa.
Kotun ta kuma bayyana ƙarar a matsayin “wata hanya ta amfani da kotu ba bisa ka’ida ba”, tare da yin watsi da buƙatar da mai ƙarar ya gabatar na a cire mai shari’ar daga sauraron shari’ar.
Johnmary Jideobi ya shigar da ƙarar ne yana mai hujjar cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya hana duk wanda aka rantsar sau biyu a matsayin shugaban ƙasa sake tsayawa takara.
Sai dai lauyoyin Jonathan da na Babban Lauyan Tarayya sun bayyana ƙarar a matsayin mara tushe da kuma yunƙurin hana tsohon shugaban ƙasar shiga siyasa ta hanyar amfani da kotu.
A yayin da ake ci gaba da hasashe kan yiwuwar Jonathan zai tsaya takara a 2027, har yanzu tsohon shugaban ƙasar bai fito fili ya tabbatar ko ya musanta aniyarsa ba.
Sai dai a kwanakin baya, wani ɓangare na jam’iyyar PDP mai alaƙa da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana Jonathan a matsayin ɗan takararsu na shugaban ƙasa a 2027.