NUJ ta sauke shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai na jihar Jigawa

0 154

Kungiyar ’Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta sanar da sauke Comrade Zangina Mohammed Kura daga kujerarsa ta shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta jihar wato Correspondents’ Chapel, nan take ba tare da bata lokaci ba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na jiha, Comrade Ismail Ibrahim, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta bayyana cewa an dauki matakin ne bayan korafe-korafe da kuma hujjojin da suka nuna cewa Comrade Zangina Mohammed Kura ya tsunduma cikin harkokin siyasa ta hanyar neman takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar mazabar Kura/Garin Malam karkashin jam’iyyar ADC.

Kungiyar ta ce shiga harkokin siyasa ga dan jarida ya saba wa dokokin aikin jarida tare da rage martaba da kima na aikin, inda ta jaddada cewa dokar NUJ ta tanadi cewa dole ne duk dan kungiyar da zai shiga siyasa ya sauka daga mukaminsa kafin fara harkokin siyasa.

Saboda haka, kungiyar ta umarci Comrade Zangina Mohammed Kura da ya gaggauta mika duk wasu kayayyakin kungiyar ga mataimakinsa.

Hakazalika, kungiyar ta bukaci ma’aikatu, hukumomin gwamnati, kungiyoyi da jami’an tsaro da su daina mu’amala da shi a matsayin shugaban Correspondents’ Chapel na Jihar Jigawa.

Leave a Reply