Akalla Alhazai milyan 2 ne suka fita Mina domin gudanar da Hajjin 2026

0 149

Akalla alhazai miliyan biyu daga sassa daban-daban na duniya ne a Mina suka gudanar da ibadar Hajjin bana ta 2026.

Fuskokin mahajjatan cike suke da farin ciki da ƙanƙan da kai yayin da suke barin masaukansu a birnin Makka zuwa Mina, domin manyan ibadun Hajji.

Maza na sanye da fararen tufafin harami, yayin da mata ke cikin tufafin da suka rufe jikinsu yadda addini ya tanada, suna masu yawaita ambaton “Labbaikallahumma Labbaik” cikin nutsuwa da ibada.

Mahukuntan Saudiyya sun ɗauki matakan tsaro da kula da lafiyar mahajjata domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali da tsari.

Leave a Reply