Trump Ya Aike Wa Tinubu Wasiƙa, Ya Yaba da Ƙwazon Gwamnatinsa Wajen Yaƙi da Ta’addanci

0 59

Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya aike wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wasiƙar yabo, inda ya jinjinawa jagorancinsa da ya bayyana a matsayin mai ƙwazo da jajircewa wajen jagorantar Najeriya da yaƙi da ta’addanci.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.

A cikin wasiƙar, Trump ya yaba da ƙudurin Tinubu na magance matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman tashe-tashen hankula da hare-haren ta’addanci da ke shafar wasu al’ummomi.

Ya ce:

“Na gode da wasiƙarka mai cike da tunani. Kalmominka masu kyau sun yi matuƙar tasiri a gare ni, kuma ina yaba da jajircewar jagorancinka wajen yi wa al’ummar Najeriya hidima.”

Trump ya ƙara da cewa:

“Ina yaba da ƙudurinka na magance matsalolin da ke addabar ƙasarka, musamman rikice-rikicen da ke shafar al’ummomi. Babbar girmamawa ce gare ni in kasance tare da kai wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da kuma ƙarfafa Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ta zama mafi ƙarfi da wadata.”

Sanarwar ta bayyana cewa alaƙar Najeriya da Amurka ta ƙara ƙarfi a baya-bayan nan, musamman a fannin tsaro.

A watan Nuwamban bara, Trump da Tinubu sun amince da kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa kan Tsaro, wanda Mashawartan Tsaro na ƙasashen biyu ke jagoranta.

Ta hanyar wannan haɗin gwiwa, an cimma yarjejeniyoyi kan horas da jami’an tsaro, musayar bayanan sirri da kuma gudanar da ayyukan haɗin gwiwa domin yaƙar ta’addanci.

Sanarwar ta ce haɗin gwiwar ya taimaka wajen harin haɗin gwiwa da aka kai a ranar 16 ga Mayu kan maboyar mayaƙan ISIS a yankin Tafkin Chadi, wanda ya yi sanadin kashe babban jagoransu, Abubakar Al-Minoki, tare da wasu manyan kwamandojinsa.

Haka kuma, a makon da ya gabata, Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afirka, Frank Garcia, ya kai ziyara Abuja, inda ya gana da manyan jami’an gwamnatin Najeriya tare da jaddada aniyar ƙasashen biyu na ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa a fannonin tsaro da sauran muhimman fannoni.

Leave a Reply