Hisbah Ta Gargadi Masu Neman Shiga Shirin Auren Gata Kan Masu Damfara
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta gargadi jama’a da kada su biya kuɗi ga duk wanda ya yi iƙirarin zai taimaka musu wajen yin rajista ko samun gurbi a shirin Auren Gata, tana mai bayyana cewa irin waɗannan buƙatu damfara ce.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ne ya yi wannan gargaɗi a Kano ranar Laraba.
Ya ce hukumar ta samu rahotannin cewa wasu mutane na karɓar kuɗi daga masu son cin gajiyar shirin, duk da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ɗaukar nauyin shirin gaba ɗaya.
Dr. Aminuddeen ya jaddada cewa Hisbah ko Gwamnatin Jihar Kano ba su ba wa kowa izinin karɓar kuɗin rajista ko wani nau’in kuɗi daga masu neman shiga shirin ba.
Ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince gwamnati ta ɗauki cikakken nauyin shirin, wanda ya haɗa da:
Kayan aure,
Kayan ɗaki,
Kuɗin jigilar kayan ɗaki,
Da kuma jarin fara sana’a ga ma’auratan.
A cewarsa, shirin kyauta ne gaba ɗaya, don haka ya buƙaci masu neman shiga su yi watsi da duk wanda ke neman kuɗi ko alkawarin samar musu da gurbi a madadin kuɗi.
Ya kuma yi kira ga duk wanda aka damfara ko aka nemi ya bayar da kuɗi da ya kai rahoto ga Hukumar Hisbah ko jami’an tsaro domin a binciki lamarin tare da hukunta masu laifi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shirin Auren Gata na bana zai haɗa ma’aurata 1,500, inda gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 1.5 domin gudanar da shirin.
An kuma bayyana cewa shirye-shiryen gudanar da auren sun yi nisa, ciki har da gwaje-gwajen lafiya da sauran tsare-tsaren da ake buƙata, kafin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ranar da za a ɗaura auren.