An daure masu gadi biyu rai-da-rai kan yi wa yarinya mai shekara 6 fyade a Abuja

0 19

Wata babbar kotun Abuja ta yanke wa wasu masu gadi biyu, James Sule da Adamu Yau, hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan samunsu da laifin yi wa wata yarinya mai shekara shida fyade na tsawon shekaru shida.

Hukumar NAPTIP ta bayyana cewa an kama mutanen ne bayan yarinyar ta tona asirin cin zarafin da ake yi mata tun daga shekarar 2016 a unguwar Lugbe da ke Abuja.

Rahotanni sun ce waɗanda aka yankewa hukuncin suna yi wa yarinyar barazanar kashe ta da iyayenta idan ta sanar da kowa abin da suke aikatawa.

Kotun ta yanke musu hukuncin ne ba tare da zabin tara ba, yayin da aka ce wani mutum na uku da ake zargi da hannu a lamarin ya gudu.

Shugabar NAPTIP, Binta Bello, ta yaba wa kotun bisa hukuncin, tana mai cewa hakan zai zama darasi ga masu aikata irin wadannan laifuka.

Leave a Reply