Jihar Jigawa Ta Kashe Naira miliyan 700 Don Mayar da Yara Makaranta

0 404

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kashe fiye da Naira miliyan700 cikin kasa da shekaru biyu don mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta cikin ajinsu, a wani yunkuri na karfafa ilimi da bunkasa hazakar al’umma.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin ganawa da shugabannin Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) na Zone A, inda ya jaddada kudurinsa na ganin ilimi wani muhimmin jari ne ga ci gaban kasa, tsaro da tattalin arziki.

Gwamnan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kafa tsarin NELFUND, wanda ke taimakawa dalibai wajen biyan kudin makaranta da rage barazanar ficewar su daga makaranta. Haka kuma, jihar ta taimaka wa dalibai marasa karfi da kusan Naira Miliyan 700 ta ofishin harkokin dalibai.

Shugabannin NANS sun yi maraba da wannan tallafi, suna mai cewa matakin gwamnati ya nuna kyakkyawan shugabanci wanda ke sauraron bukatun dalibai.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da ci gaba da tallafa wa ilimi da samar da yanayi mai kyau don karfafa kwazon dalibai da bunkasa makomar jagoranci a kasar.

Leave a Reply