Guguwar Iska Ta Kashe Mutane Uku, Ta Lalata Gidaje Da Ababen More Rayuwa A Yobe

0 43

Guguwar Iska Ta Kashe Mutane Uku, Ta Lalata Gidaje Da Ababen More Rayuwa A Yobe

Aƙalla mutane uku ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wata mummunar guguwar iska da ta afkawa garin Gashua, hedikwatar ƙaramar hukumar Bade a jihar Yobe.

Mazauna garin sun ce guguwar, wadda ta ɗauki kusan mintuna 30 a yammacin ranar Laraba, ta lalata daruruwan gidaje da shaguna, tare da rusa hasumiyoyin sadarwa da sandunan wutar lantarki, lamarin da ya bar iyalai da dama ba tare da matsuguni ba tare da jawo asarar dukiyoyi ta miliyoyin nairori.

Wani mazaunin garin mai shekara 65, Aminu Muhammad, ya bayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin munanan bala’o’in da ya taɓa gani a rayuwarsa.

Ya ce mutane uku sun mutu, yayin da gidaje da hanyoyin samun abin masarufi na mutane da dama suka lalace.

Muhammad ya danganta tsananin barnar da sare bishiyoyi ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa hakan ya sa yankin ya fi fuskantar barazanar iska mai ƙarfi.

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Abdulhadi Ibrahim Gashua, ya ce guguwar ta ƙwace rufin gidansa, ta lalata motarsa da kuma na’urorin hasken rana (solar panels) da ke saman gidan.

Shi ma wani mazaunin garin, Yahaya Mato, ya ce duk da cewa ruwan saman bai yi ƙarfi sosai ba, guguwar iskar ce ta haddasa babbar barna, inda ta lalata gidaje tare da rusa wasu hasumiyoyin sadarwa.

Ya bayyana cewa sare bishiyoyin da ke hana iska ƙarfi saboda noma da faɗaɗa unguwanni ya ƙara jefa yankin cikin haɗarin irin wannan bala’i.

Shugaban ƙaramar hukumar Bade, Ibrahim Babagana Yurema, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce guguwar ta fara ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin Laraba kuma ta ɗauki kusan rabin sa’a.

Ya ce mutane uku sun mutu, yayin da wasu ke karɓar magani a Asibitin Kwararru na Gashua, inda aka sallami wasu daga cikinsu bayan sun samu sauƙi.

Ya ƙara da cewa kusan kowane mazaunin Gashua ya fuskanci wata irin asara sakamakon guguwar.

A nasa ɓangaren, Daraktan Bincike da Ceto na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA), Dakta Ibrahim Muhammad Jalo, ya ce tuni hukumar ta fara tantance irin barnar da guguwar ta yi a yankunan da abin ya shafa.

Ya bayyana cewa guguwar ta kuma shafi wasu sassan ƙananan hukumomin Yunusari da Bursari, inda aka tura jami’an agajin gaggawa domin tantance buƙatun waɗanda abin ya shafa.

Jalo ya tabbatar da cewa bayan kammala tantancewar, gwamnatin jihar za ta fara rabon agajin gaggawa ga iyalan da suka fi buƙata, bisa umarnin Gwamna Mai Mala Buni.

Leave a Reply