Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Takwas, Sun Kwato Makamai A Katsina

0 39

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Takwas, Sun Kwato Makamai A Katsina

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda takwas tare da ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da babura biyar a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Rundunar sojin ta ce an gudanar da farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa wasu ‘yan ta’adda masu biyayya ga fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Idi Abasu Aiki, na shirin tare hanyar Kakumi zuwa Guga domin kai hare-hare kan matafiya.

A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Brigade ta 17, Kyaftin Abayomi Adisa, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi wa maharan kwanton ɓauna a kan hanyar.

Ya ce yayin da ‘yan ta’addan ke tafiya a kan babura biyar, dakarun sojin suka buɗe musu wuta, lamarin da ya yi sanadin kashe takwas daga cikinsu.

Bayan kammala artabun, jami’an tsaron sun binciki yankin inda suka ƙwato bindigogi AK-47 guda biyu da baburan da maharan ke amfani da su.

Sanarwar ta ƙara da cewa an miƙa makaman da baburan da aka ƙwato ga rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Bakori domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.

Haka kuma, rahotannin sirri sun nuna cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hare-haren ramuwar gayya kan al’ummomin Kakumi, Guga, Unguwan Dan Shuni, Kwai da sauran ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Bakori.

Saboda haka, rundunar sojin ta ce dakarun da ke sansanonin Forward Operating Bases (FOBs) na Ruwan Godiya da Mabai sun ƙara kaimi wajen sintiri da mamaye yankunan da ake zargin maharan za su bi, domin hana su samun damar kai hari tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Rundunar ta tabbatar da cewa jami’an tsaro na ci gaba da sa ido sosai kan lamarin, tare da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana domin dakile duk wani sabon hari a yankin.

Leave a Reply