Gwamnan Zamfara: Na Ƙi Biyan Kuɗin Fansa Naira Miliyan 300, Na Ce Su Kashe ‘Yan Uwana

0 36

Gwamnan Zamfara: Na Ƙi Biyan Kuɗin Fansa Naira Miliyan 300, Na Ce Su Kashe ‘Yan Uwana

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ya ƙi biyan kuɗin fansa na Naira miliyan 300 da masu garkuwa da mutane suka buƙata bayan sun sace ‘yan uwansa a shekarar 2019.

Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne saboda ya yi imanin cewa biyan kuɗin fansa na ƙara ƙarfafa masu garkuwa da mutane su ci gaba da aikata laifukansu.

Lawal ya bayyana haka ne a wajen taron ARISE News da THISDAY Townhall da aka gudanar a Abuja, inda ya kuma sake jaddada buƙatar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi domin inganta yaƙi da matsalar tsaro.

Ya ce lokacin da aka sace ‘yan uwansa, masu garkuwar sun nemi a biya su Naira miliyan 300, amma ya ƙi yin wata tattaunawa da su ko biyan ko sisi.

A cewarsa, “An sace ‘yan uwana a shekarar 2019, suka nemi Naira miliyan 300. Na ce ba zan biya ko sisi ba. Idan suna so, su kashe su.”

Ya ƙara da cewa duk da ƙin biyan kuɗin fansa, daga bisani masu garkuwar sun saki ‘yan uwansa bayan sun shafe kusan watanni uku a hannunsu.

Gwamnan ya ce wannan ƙwarewar ta ƙara tabbatar masa da cewa biyan kuɗin fansa na ƙarfafa masu aikata laifuka su ci gaba da sace mutane.

Ya jaddada cewa ba zai taɓa yin sulhu da masu garkuwa ko biyan su kuɗin fansa ba, komai ya faru.

Lawal ya kuma yi kira da a kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa gwamnoni na da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, amma ba su da ikon ba da umarni ga jami’an tsaro da ke aiki a jihohinsu.

Ya ce tsarin tsaron da ake da shi a yanzu na sanya gwamnoni cikin mawuyacin hali, domin ana ɗora musu alhakin matsalar tsaro alhali ba su da cikakken iko kan hukumomin tsaro.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin Zamfara na ɗaukar fiye da kashi 30 cikin 100 na kuɗaɗen ayyukan tsaro a jihar, inda ta samar da motocin aiki sama da 500 ga jami’an tsaro, tare da ba su motoci masu sulke (APCs da MRAPs) guda 35.

Haka kuma, ya ce gwamnatin jihar ta sayo jiragen sama marasa matuƙa (drones) na sa ido da kuma na yaƙi domin taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙar ‘yan bindiga.

A ƙarshe, Lawal ya ce mafita ga matsalar tsaron Najeriya ita ce ƙarfafa hukumomin tsaro ta hanyar inganta kuɗaɗen gudanarwa, walwalar jami’ai, horaswa da amfani da fasahar zamani, maimakon yin sulhu ko biyan kuɗin fansa ga masu aikata laifuka.

Leave a Reply