Bala T.O yayi kira ga yan siyasa su taimakawa mata da jarin da kuma sana’o’i domin inganta rayuwar su

0 580

Shugaban karamar hakumar Hadejia yayi kira ga yan siyasa su taimakawa mata da jarin da kuma sana’o’i domin inganta rayuwar su.

Ya ce akwai bukatar a rika fifita al’amuran mata lura da irin gudunmawar da mata suka bayar lokacin yakin neman zabe da lokacin zabe, ta hanyar sanya su cikin shirye-shiryen koyar da sana’o’i da bayar da jari domin cigaban al’umma baki daya.

Alhaji Abdulkadir Umar T.O ya bayyana haka ne lokacin da wata kungiyar mata masu goya masa baya ke karrama shi da safiyar jiya juma’a.

Da yake jawabi ya godewa kungiyar matan bisa kwarin guiwa da shawarwari suke bashi, wajen sauke nauyin shugabancin al’ummar karamar hakumar Hadejia.

Haka kuma yayi alkawarin tallafawa mata 120 da jari domin dogaro da kansu.

Kazalika, ya ce akwai yiyuwar karamar hakumar zata bullo da shirin aurar da zawarawa da ‘yan mata masu karamin karfi, tare da sanya dokar takaita lefe da kayan aure a wani yunkuri na daidaita yanayin tsadar aure. Tun da farko yan kungiyar sun lura da aikin da Abdulkadir Umar T.O ke gudanarwa a fadin karamar hakumar inda suka ce wannan ne ya basu kwarion guiwar shirya biki domin karrama shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: