Muddin Isra’ila bata daina kai hare-hare gaza ba, yaki zai barke a Gabas ta Tsakiya baki daya

0 363

Shugaban kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, Hassan Nasrallah ya gargadi kasar Amurka cewar muddin Isra’ila taki daina kai munanan hare hare a Gaza, fafatawar da ake yi a iyakar Lebanon zai rikide zuwa yakin Gabas ta Tsakiya baki daya. 

Kungiyar Hezbollah ta kwashe shekaru tana fafata yaki da Isra’ila a kan iyakar da suka yi da juna tun bayan kazamin yakin da suka gwabza a shekarar 2006. 

Yayin gabatar da jawabin da aka yada ta kafar talabijin, wanda shine irinsa na farko tun bayan barkewar yaki tsakanin Hamas da Isra’ila, Nasrallah yace a shirye su dauki mataki dangane da duk wani abinda ka iya faruwa. 

Shugaban ya zargi Amurka a kan yakin dake gudana a Gaza da kuma yawan adadin fararen hular da suka mutu, inda ya bukaci kawo karshen rikicin a yankin da aka yiwa kawanya domin kaucewa fadadan yakin. 

Nasrallah yace Hezbollah bata jin tsoron sojojin ruwan Amurka da aka girke a yankin tun bayan barkewar yakin. 

Shugaban yace ci gaba da yakin da ake yi da kungiyar Hamas, wadda babbar kawace a gare su, na gudana ne tun bayan harin da mayakan Hamas suka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Octoba, yayin da yake cewa suna ci gaba da nazari a kan abinda ke gudana da kuma matakan da zasu dauka nan gaba.  Rundunar sojin Isra’ila tace sojojin ta na can suna fafatawa ta gaba da gaba da mayakan Hamas a titunan Gaza, a yukunrin su na kawar da kungiyar Hamas daga yankin baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: