EFCC ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da damfara ta intanet a jihar Ribas

0 184

Jami’an Hukumar yaƙi da cin hanci da rahsawa EFCC na shiyyar Fatakwal sun kama wasu mutane 26 da ake zargi da damfara ta intanet a ta wuraren gidan talabijin na kasa da Choba na Fatakwal, a jihar Ribas.

Hukumar EFCC ta bayyana haka ne a shifin na X cewa an kama su ne biyo bayan sahihan bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na hannu a ayyukan da suka shafi intanet.

Kayayyakin da aka ƙwace daga hannun su dai sun haɗa da wayoyi daban-daban da kwamfutoci da manyan motoci guda shida.

Za a kuma gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: