Wata Kungiya mai zaman kanta ta yi aikin jinya ga mata manoma 200 a jihar Jigawa

0 205

Wata Kungiya mai zaman kanta ta Rashak Farms and Agro Allied Limited ta yi aikin jinya ga mata manoma 200 a kananan hukumomin Hadejia da Mallam Madori a jihar Jigawa.

Da take kaddamar da shirin a garin Hadejia shugabar hukumar Rashak Farms da Agro Allied Limited, Rahmah Aderinoye ta bayyana cewa, an tsara manufar wayar da kan likitocin ne domin samar da kiwon lafiya da kuma inganta rayuwar mata manoma baki daya.

Kodayake kungiyar Agro Allied Organisation  tace samar da manoma ma koshin lafiya zai samar da girbi mai yawa don inganta wadatar abinci a kasar.

Shugabar wanda ya samu wakilcin Manajan Impact and Innovation Adeola Balogun, shugaban ya bayyana cewa, kungiyar ta RASHAK ta hanyar shirye-shiryenta na samarwa mata masu noma kudaden shiga da kuma samun damar shiga kasuwanni, wanda hakan ya basu damar kara yawan aiki da inganta rayuwarsu.

Ko’odinetan RASHAK na jihar Jigawa Ahmad Nagwamitse ya sanar da matan manoma da su kara sa samun tallafi daga Rashak kuma su kasance a shirye don fadada sana’ar noma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: