Kotu ta hukunta Ramat Mba bisa laifin yin jabun sa hannun Marigayi Abba Kyari

0 114

Wata babbar kotu da ke zamanta a  birnin tarayya a Abuja, ta hukunta wata mata da ake kira Ramat Mba, mai ‘ya’ya biyar, bisa laifin yin jabun sa hannun tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Marigayi Abba Kyari.

Alkalin kotun, Mai shari’a Ibrahim Mohammad, ya dage yanke hukuncin zuwa ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu, 2024, amma ya bayar da umarnin a tsare ta a gidan yari na Suleja.

Takardu da aka gabatar, sun nuna cewa wanda ake tuhumar ta yi damfara ne da wata takarda ta ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa zuwa ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari da kuma sa hannun sa.

Wasikar, wacce aka aike wa shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran lafuka na ICPC.

Sai dai kuma, Marigayi Shugaban Ma’aikatan, a wata rubutacciyar wasika da aka gabatar a gaban kotu a matsayin baje kolin, ya nisanta kansa ko ofishinsa daga ba da izinin wannan wasikar.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Ibrahim Muhammad, da laifuka 1, 2, 3 da 5 da suka shafi zamba da jabu yayin da aka sallame ta a kan shari’a 4 da ke da alaka da aikata laifuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: