Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta kubutar da wasu fasinjoji 17 da aka sace a jihar Katsina

0 86

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta kubutar da wasu fasinjoji 17 da aka sace galibinsu maza daga hannun ‘yan ta’adda a yankin Solar General da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.

Ya ce rundunar sojojin ta 9 tare da hadin guiwar rundunar ‘yan sandan Katsina, da jami’an tsaro na al’umma na jiha, da mafarauta na musamman, da mafarauta na garin Batsari, a dalilin haka kuma cikin gaggawa aka tura su wurin.

Da isar jami’an tsaro na hadin guiwar sun yi artabu da ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su, inda suka yi watsi da mutanen da suka yi garkuwa da su, suka tsere zuwa cikin daji da ke kusa da wurin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, babban sakataren yada labarai na gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya bayyana cewa sojojin na ci gaba da aiki tukuru a yankin na jihar Katsina domin dakile ci gaba da aikata miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron mazauna yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: