An kara kama masu alaka da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami’ar Texas
An samu karin kama masu alaka da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a wasu wurare, a wannan karon a jami’ar Texas da ke Dallas.
An ba su takardar sanarwa a rubuce inda aka gargade su da su tashi kafin ‘yan sanda su dirauwa sansanin.
Da misalin karfe 5:00 a ranar Laraba, ‘yan sanda sun ce an kama mutane 17 da laifin aikata laifuka.
Sai dai CBS ta ruwaito cewa adadin ya kai 21, in ji lauyoyin da ke kare wadanda ake tsare da su.