Kungiyar Kwadago ta kasa, ta fitar da gargadi kan duk wani yunkuri na tauye hakkin ‘yan Najeriya na bayyana ra’ayoyinsu, musamman dangane da zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.
Kungiyar kwadagon ta kuma yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya saurari kukan ‘yan Najeriya kan yunwa da wahalhalun da kasar ke fama da su.
An shirya wani bangare na ‘yan Najeriya don fara zanga-zanga a fadin kasar a ranar 1 ga watan Agusta mai taken #TinubuMustGo da #Revolution2024.
Fadar shugaban kasar, ta bayyana irin wadannan kiraye-kirayen a matsayin cin amanar kasa, ta kuma zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da magoya bayansa da yada zanga-zangar.
A cikin wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya yi zargin cewa wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar ba ‘yan dimokradiyya ba ne, ‘yan mulkin kama karya ne.