Yariman Saudiyya ya tattauna da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho

0 177

Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya tattauna da shugaban Rasha, Vladimir Putin ta wayar hannu.

Manema labarai sun ruwaito cewa shugabannin biyu sun tattauna yadda za su kulla dangantaka tsakankin ƙasashen biyu, tare da yadda za su samar wa ƙasashen ci gaba ta fannoni daban-daban.

Ƙasashen Rasha da Saudiyya na cikin ƙasashe mafiya arzikin man fetur a duiya.

Shugaban Rasha dai na ƙoƙarin kulla ƙawance da ƙasashen yankin Asiya, bayan dangantaka tsakanin ƙasarsa da ƙasashen Yamma tayi tsami kan batun yaƙin Ukraine.

Leave a Reply

%d bloggers like this: