Sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu yayi ne ya fardado da Najeriya daga durkushewa

0 61

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu ya yi a shekara daya ya fardado da kasar nan daga durkushewa.

Ya bayyana tsare-tsaren a matsayin wadanda suka wajaba idan aka yi la’akari da halin da Najeriya ke ciki na kangin talauci a lokacin da Tinubu ya karbi mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Ya bayyana dalilin da ya sa gwamnati tayi fatali da tsarin biyan tallafin man fetur da kuma shiga cikin tsarin hada-hadar chanjin kukdade, inda ya ce shugaban kasa ya zabi wannan hanya ne domin dai-daita tattalin arzikin kasa.

Shettimma ya roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri da sauye-sauyen gwamnatin yana mai tabbatar da cewa Tinubu akawai kalubale mai yawa da wannan gwamnati taci karo dasu a lokacin da suka karbi ragamar mulkin kasar nan.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa matakan da aka dauka zuwa yanzu za su samar da sakamakon da ake bukata ga al’ummar kasar nan, nan da wani dan lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: