Shugaba Tinubu zai halarci taron kasashen Larabawa da Afirka a Kasar Saudiyya

0 217

Shugaban kasa Bola Tinubu, zai kai ziyara birnin Riyadh na Kasar Saudiyya domin halartar taron kasashen Larabawa da Afirka a ranar 10 da 11 ga watan nan na Nuwamba.

Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, ya ce a yayin taron, Tinubu zai tattauna kan batutuwa da suka shafi huldar tattalin arziki tsakanin yankunan da harkar noma da kuma yaki da ta’addanci.

A cewar hadimin shugaban kasar, halartar taron wani yunkuri ne na  bunkasa tattalin arzikin Najeriya da kuma jawo hankalin kasashen waje.

Ngelale ya ce a matsayin Tinubu na shugaban hukumar gudanarwar Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) zai kasance kan gaba a taron wajen bayar da shawarwarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen yankuna biyu. Sauran su ne batun inganta harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin Saudiyya da nahiyar Afirka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: