Dakarun Operation Hadarin Daji sun fatattaki yan bindiga a Jihar Zamfara

0 198

Dakarun Operation Hadarin Daji dake yaki da ta’adanci a yankin Arewa maso yammacin kasar, sun fatattaki yan bindiga a Jihar Zamfara a wani kwanton bauna da suka yiwa yan ta’addar.

Dakarun sun kuma samu nasarar lalata wani hari da yan bindigar suka yi yunkurin kaiwa a Kauyen Karazau dake karamar hukumar Bungudu a Jihar ta Zamfara.

A cewar wata sanarwa daga kakakin rundunar Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, dakarun sun samu kiran gaggawa cewa yan bindiga masu yawan gaske sun kai harin Kauyen na Karazau.

Yace dakarun sunyiwa yan bindigar kwanton bauna. Sanarwar ta kara da cewa, dakarun sun kuma mamaye yankin domin kare mazauna yankunan daga hare-haren yan bindiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: