Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammad ya kaddamar da aikin titi na kudi kimanin N10Bn

0 186

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammad, ya kaddamar da aikin titi mai hannu biyu mai nisan Kilo Mita 11 a daga Ningi zuwa Gudduba kan kudi kimanin Naira Bilyan 10.

Da yake jawabi yayin kaddamar da aiki, Gwamnan Jihar yace an kammala aikin hanyar, kuma zata inganta tattalin arzikin yankin dama Jihar baki daya.

Gwamnan ya bayyana cewa hanyar tana da matukar Alfano, domin za’ana amfani da ita wajen gudanar da kasuwanci a yankin arewacin kasar nan, kuma zata rage yawaitar haddura da ake samu wanda yake sanadiyyar rayuka da dukiyoyin mutane.

Gwamna Bala Muhammad ya fadawa mutanen Ningi da jihar Bauchi baki daya cewa,hanyar zata kawo cigaba sosai a fannin sufuri, inda ya bukaci mutanen jihar da su baiwa gwamnatin sa goyan bayan domin samun cigaba.

A nasa jawabin sarkin Ningi Alh Muhammad Yunusa Dan Yaya, ya yabawa gwamnan jihar bisa wannan aiki da ya musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: