Mayakan Boko Haram sun kashe manoma 13 a yankin Mafa dake Jihar Borno

0 158

Akalla manoma 13 aka kashe wasu da dama suka jikkata sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a yankin Mafa dake Jihar Borno.

An rawaito cewa Mayakan na Boko Haram sun mamaye gonakin shinkafa yayinda manoma ke aiki a gonakin su, inda suka yi ta musu yankan rago.

A cewar dakarun sa kai, mutane 13 aka gano sun mutu yayin da ake cigaba da neman wadanda suka bata.

Majiyoyi sun ce mayakan sun je garin ne Ayari uku akan Babura kafin su fara farmakar manoman. Kazalika, an rawaito cewa ‘Yan Boko Haram din sunyi amfani da adduna da wukake yayin kashe Manoman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: