Tsohon sakataren jam’iyyar PDP na kasa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

0 137

Tsohon sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Abubakar Mustapha, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna.

Ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar ne ta wata wasika da ya aike wa shugaban gundumar Gubuchi da ke karamar hukumar Makarfi a jihar mai kwanan wata 15 ga Yuli, 2024.

A cewar sanarwar da aka rabawa manema labarai a Kaduna jiya Lahadi, ya bayyana cewa bisa radin kansa ya yi murabus daga jam’iyyarsa ta PDP saboda wasu dalilai na kashin kansa.

Bako, wanda kuma ya mika takardar murabus dinsa zuwa ga shugaban gundumar Shaba a karamar hukumar Kaduna ta Arewa ya bayyana dalilan ficewa daga jam’iyyar.

Wasu daga cikin dalilan da ya bayyana sun hada da rashin mayar da hankali da alkibla, cece-kuce, da kuma rikon amana a cikin dalilan da ya sa ya fice daga jam’iyyar. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: