An kaddamar kidayar dabbobi a jihar Jigawa
Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasa reshen jihar Jigawa tare da hadin gwiwar kungiyar Fulani ta kasashen Afrika ta yamma mai suna RPF sun kaddamar da aikin kidayar dabbobi a jihar Jigawa.
Shugaban kungiyar Kautal Hore na jjihar Jigawa, Umar Kabiru Dubantu ya sanar da hakan a lokacin ganawa da wakilinmu.
Yace an fara aikin kidayar dabbobin ne a ranar asabar Hudu ga wata a kan hanyoyin mota na Adare zuwa Galadi ta bi ta Maigatari ta wuce zuwa Birniwa zuwa Bursali.
Umar Kabiru Dubantu yana mai cewar za a shafe tsawon watanni uku ana kidayar da nufin tabbatar da ganin an kidaya dabbobin domin samar musu da makiyayu da kuma ciyawa.
Yace aikin kidayar ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin gwamnatin jihar Jigawa da kuma jamhuriyar Nijar A cewarsa aikin idan an kammala zai taimaka wajen inganta zaman lafiya da samun bayanan dabbobin da Fulani suke dasu da kuma kyautata dangantaka a tsakanin Zindar da Nigeria.