Za’a farfado da ayyukan kungiyoyin taimakon kai da kai a jihar Jigawa

0 193

Ma`aikatar lura da kananan hukumomi ta jihar Jigawa tace zata farfado da ayyukan kungiyoyin taimakon kai da kai domin marawa kudurin gwamnati baya na tsaftar mahalli.

Daraktan lura da ayyukan gayya na ma`aikatar, Alhaji Baita Saleh ne ya bayyana haka lokacin da masu taimakawa gwamna na musamman akan kungiyoyin sa kai suka ziyarci karamar hukumar Birnin kudu a cigaba da rangadin kananan hukumomin jihar nan.

Yace suna rangadin kananan hukumomin ne domin kara zaburar da kananan hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu wajen gudanar da ayyukan taimakon kai da kai.

Alhaji Baita Saleh ya bayyana muhimmancin dashen bishiyoyi da kum renon su har su girma, inda yace ma`aikatar zata dawo da ayyukan kula da kungioyoyi masu zaman kansu.

A jawabansu daban daban mataimaka na musamman ga gwamna, Alhaji Garba A Abdullahi da Labaran Musa sun jaddada bukatar dake akwai ga kungiyoyi wajen baiwa gwamnati hadin kai da goyon baya wajen kula da tsaftar mahalli.

Leave a Reply

%d bloggers like this: