Hukumar STOWA zata fara rangadi shiyoyin hukumar guda bakwai daga mako mai zuwa

0 145

Hukumar samarda ruwansha a kananan garuruwa ta jihar Jigawa STOWA zata fara rangadi shiyoyin hukumar guda bakwai daga mako mai zuwa

Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Adamu Garba ya sanar da hakan ga wakilinmu ta wayar hannu.

Yace tawagar hukumar da ta kunshi mai baiwa gwamna shawara da kuma masu taimakawa gwamna kan aiyukan hukumar guda biyu da shi kansa da kuma sauran Daraktoci zasu ziyarci shiyoyin hukumar domin gani da ido aiyukan shiyoyin da kuma gidajen ruwa

Injiniya Adamu Garba ya kara da cewar tawagar zata fara rangadin ne da shiyyar Birnin Kudu daga ranar Litinin 20 ga wata

A cewarsa bayan dubawa da kuma tantance irin abubuwan da suka gami, zasu rubuta cikakken rahoto ga gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: