Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu dalibai mata biyu na kwalejin kimiyya da fasaha da ke Tsafe a jihar Zamfara.
An sace daliban ne a daren Alhamis a wani gidan haya a unguwar Matuna, a wajen garin.
An ce ‘yan bindigar sun kai farmaki yankin ne da nufin yin garkuwa da mutanen amma suka yi awon gaba da daliban.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban kwalejin, Hamisu Yelwa, ya ce hukumomin makarantar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro sunyi hadaka domin fito da cikakken bayanin abin da ya faru.
Yelwa ya ce an tsaurara matakan tsaro a kusa da makarantar da kuma yankunan makota.