Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya ta fara sayar da takardar sheda na shekarar 2024

0 271

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya a ranar Juma’a ta fara sayar da takardar sheda na shekarar 2024 da za ta ba da damar shiga filayen jiragen sama 24 na tarayyar Najeriya.

A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya raba wa manema labarai a Abuja, Hukumar ta ce sayar da takardar shedar ta yi daidai da umarnin shugaban kasa da majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shi.

A cewarsa, taron ya ba da umarnin cewa duk masu amfani da filayen jiragen sama na tarayya a fadin kasar nan su biya kudaden a bakin kofa.

Shugaban hulda da jama’a na filin jirgin saman Nnamdi Azikwe Mista Francis Ajaguna, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar nan cewa mutane da dama sun zo filin jirgin sun sayi takardun shedar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: