Najeriya kasa ce mai aminci ga masu saka hannun jari – Bola Tinubu

0 183

Shugaba Bola Tinubu, ya ce Najeriya ta kasance kasa mai aminci ga masu saka hannun jari, inda yace sabon tsarin hako ma’adinan zai kasance wata hanya ta samar da kudaden shiga a kasar nan.

Shugaban ya kuma yi alkawarin cewa a ko da yaushe gwamnatin sa za ta bayar da tallafin da ake bukata domin ganin an samu ci gaba a harkokin kasuwanci a kasar nan.

A yayin da yake jawabi a lokacin da ya karbi tawagar shugaban wani kamfanin gina layin dogo na kasar Sin Mista Dai Hegen, a fadar gwamnati a jiya  Juma’a, Tinubu ya tabbatar wa shugabannin ‘yan kasuwan kasar Sin cewa jarin da suke zubawa a Najeriya zasu samu tagomashi mai kyau inda yace  gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru wajen kara karfafa yanayin kasuwanci.

Shugaban ya bayyana cewa, gwamnatinsa na maraba da damar da aka ba ta na fadada hadin gwiwar kasuwanci da kamfanin, da kuma inganta muhimman ababen more rayuwa da kayayyakin more rayuwa domin moriyar juna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: