An yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa shigo da alumma cikin tsare tsaren kasafin kudi

0 206

Kungiyar kyautatuwar zaman jama-a mai rajin shugabanci na kwarai Exceptional Leadership and Integrity Promotion Initiatives ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa shigo da alumma cikin tsare tsaren kasafin kudi

A sanarwar da Daraktan Gudanarwar kungiyar, Isa Mustapha ya sanyawa hannu tace tattaunawar kasafin kudi da Gwamna Umar Namadi ke jagoranta ya nuna a fili yadda gwamnati take bada muhimmanci ga bukatun alumma

Ta kuma yaba da kulawar da ake baiwa alumma wajen karbar bukatun da suka bukata a kasafin kudi

Kungiyar ta yi fatan gwamnati zata yi amfani da bukatun alumma wajen tsare tsare kasafin kudi da zai cimma muradin alummar jihar nan

Sanarwar ta yabawa gwamnatin jiha bisa bullo da managartan tsare tsare da zasu inganta rayuwar alummar jihar nan

Ta kuma godewa gwamnati bisa ware wani kaso wajen bunkasa kwazon maaikata da daukar aiki da kuma aiyukan mazabu.

Isa Mustapha ya kara godewa kokarin maaikatar kasafin kudi da sauran masu ruwa da tsaki bisa alakarsu da kungiyoyin kyautatuwar zaman jama-a tare dafatan hakan zai cigaba

Daga nan kungiyar ta bada tabbacin cigaba da hadin gwiwa da gwamnati da sauran hukumomin bada tallafi wajen bunkasa tattalin arzikin jihar nan

Leave a Reply

%d bloggers like this: