Gwamnan Jihar Zamfara zai rabawa wadanda hare-haren ‘yan bindiga ya shafa kayan tallafin rage radadi a jihar

0 219

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya karbi kayan tallafin rage radadi domin rabawa wadanda hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a jihar.

Gwamna Lawal ya karbi kayan ne ranar Alhamis yayin da yake ziyara Helkwatar hukumar kula da ‘yan gudun Hijira da wadanda suka rabu da muhallan su a Abuja.

Wanna na kunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan ya kafafan yada labarai Sulaiman Bala Idris ya fitar.

Sanarwa tace gwamnan ya kai ziyara ga ofishin hukumar ne domin sanin irin rawar da hukumar zata taka ga wadanda hare-haren ‘Yan bindiga ya shafa a jihar.

Gwamnan ya jaddada bukatar hadin gwiwar hukumar wajen rage radadin  da ’yan gudun hijira sama da 2000 ke fuskanta a Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: