Majalisar Wakilai ta ƙara wa’adin aiwatar da kasafin 2025 zuwa Satumba

0 290

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da tsawaita wa’adin aiwatar da ɓangaren ayyukan raya ƙasa (Capital Projects) na kasafin kuɗin shekarar 2025 da karin watanni uku, daga ranar 30 ga Yuni zuwa 30 ga Satumban 2026.

Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne a zamanta na gaggawa da Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya jagoranta a ranar Litinin.

An cimma matsayar ne bayan amincewa da wani kudiri da ke neman gyaran dokar kasafin kuɗin 2025 domin bai wa gwamnatin tarayya ƙarin lokaci wajen kammala ayyukan raya ƙasa da har yanzu ba a kammala aiwatar da su ba.

Da yake gabatar da kudirin, Jagoran Majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya bayyana cewa akwai muhimman ayyuka da dama da ke cikin kasafin kuɗin 2025 da ba a kammala aiwatar da su ba, saboda haka ya zama dole a tsawaita wa’adin domin kauce wa illa ga tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce kudirin ba ya neman canza wani sashe na kasafin kuɗin, sai dai kawai tsawaita wa’adin aiwatar da ɓangaren ayyukan raya ƙasa daga ƙarshen watan Yuni zuwa ƙarshen watan Satumba.

Shi ma Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya ce bayanan da suka samu daga kwamitin kasafi da sauran hukumomin da abin ya shafa sun nuna cewa ana ci gaba da aiwatar da wasu ayyuka, kuma suna buƙatar ƙarin lokaci kafin a kammala su.

A cewarsa, tsawaita wa’adin zai bai wa Ma’aikatu, Hukumomi da Sassan Gwamnati damar kammala ayyukan da aka ware musu kuɗi a cikin kasafin shekarar 2025.

Bayan amincewa da kudirin a karatu na biyu, majalisar ta shiga matakin nazari dalla-dalla, inda ta amince da dukkan sassan kudirin kafin daga bisani ta zartar da shi a karatu na uku a rana guda.

Matakin na nufin cewa hukumomin gwamnati za su samu ƙarin watanni uku domin ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da kuma amfani da kuɗaɗen da aka ware a kasafin shekarar 2025.

Masana na ganin cewa jinkirin aiwatar da ayyukan raya ƙasa ya kasance ɗaya daga cikin ƙalubalen da ke fuskantar tsarin kasafin kuɗi a Najeriya, lamarin da ke shafar ci gaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki.

Leave a Reply