Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin soke rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da wasu jam’iyyu huɗu bisa gazawarsu wajen cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya tanada na ci gaba da zama jam’iyyun siyasa a Najeriya.
Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a zaman kotu da ya gudana a ranar Litinin, inda ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) da ta cire jam’iyyun daga rajistar jam’iyyun siyasa a ƙasar.
Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da ADC, Accord (A), Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP) da kuma Zenith Labour Party (ZLP).
Kotun ta bayyana cewa jam’iyyun ba su cimma ƙa’idojin da doka ta tanada ba, musamman rashin samun isasshen goyon baya a zaɓen da ya gabata, ciki har da kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u da ake buƙata a wasu matakai na doka.
A hukuncin, kotun ta kuma umarci INEC da kada ta ƙyale jam’iyyun da abin ya shafa shiga duk wani zaɓe mai zuwa, ciki har da babban zaɓen 2027, matuƙar ba su cika sharuddan doka ba.
Wannan mataki na zuwa ne bayan kotun ta yi watsi da dukkan ƙorafe-ƙorafen farko da waɗanda ake ƙara suka shigar, tana mai cewa ba su da tushe na doka.
Hukuncin ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar ƙasar, yayin da ake sa ran INEC za ta bayyana matakin da za ta ɗauka kan hukuncin kotun.