Gwamnatin Jigawa zata cigaba da tallafawa Jami’ar Fasaha ta gwamnatin tarayya dake garin Babura

0 117

Gwamnatin jihar Jigawa zata cigaba da tallafawa harkokin koyo da koyar a Jami’ar Fasaha ta gwamnatin tarayya dake garin Babura.
Mataimakin Gwamnan jiha Injiniya Aminu Usman Gumel ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin sabon shugaban gudanarwar jami’ar Oba Ajigbade Gbadegesin Ogunoye Olowo na Owo na uku a ofishinsa.
Mataimakin Gwamnan wanda shugaban Ma’aikata na jiha Alhaji Muhammed K.Dagacheri ya wakilta, yace gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gina gidaje da kuma samar da kayayyakin koyo da koyarwa domin ba wa malaman jami’ar kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.
Daga nan ya bada tabbacin gwamnatin jiha na cigaba da tallafawa jami’ar domin amfanin yan jiha dama kasa baki daya.
A nasa jawabin sabon shugaban gudanarwar jami’ar basarake Oba Ajigbade ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa tallafawa jami’ar a koda yaushe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: