Wazirin Adamawa din ya ce ba zai yi ritaya daga harkokin siyasa ba kuma za a ci gaba da dama wa da shi har sai lokacin da rai ya yi halinsa.
Ya ce,” Idan wani ma yana tunanin zamu koma baya mu tsaya muna ganin yadda ake aikata rashin gaskiya da adalci ga jama’ar Najeriya to gaskiya wata kila mafarki ya ke yi, don ni ko kadan ban gaji da gwagwarmayar siyasa ba.”
Atiku Abubakar, ya ce,” A yanzu sai a saurara zuwa 2027 a gani ko zan tsaya takara ko kuma a’a.”
Wazirin Adamawar ya ce,” Dimokradiyyar nan dai mu muka yi gwagwarmayar dawo da ita don haka zamu ci gaba da tabbatar da cewa Dimokradiyya ta inganta ta samu kafuwa ina zamu zauna mu bari mu ga abubuwa na lalacewa.”
Atiku Abubakar ya tsunduma harkokin siyasa a 1989, kuma yana cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa na mulkin soji, Janar Shehu Musa Yar’adua.
Ya shiga jam’iyyu daban-daban tun da ya shiga harkokin siyasa.
An zabi Atiku Abubakar a matsayin gwamnan gwamnan Jihar Adamawa a 1998, ko da yake daga bisani Cif Obasanjo ya zabe shi domin kasancewa mataimakinsa.
Daga wancan lokacin zuwa yanzu, wannan ne karo na uku da Atiku Abubakar, ke tsayawa takarar shugaban kasa, ko da yake ya tsaya zaben fitar da gwani sau da dama.
A shekarar 2007, jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) ta tsayar da shi takara inda ya sha kaye a hannun dan takarar PDP, Umaru Musa Yar’adua.
Kazalika a shekarar 2019 ya fafata da Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC amma bai yi nasara ba.
Sai kuma yanzu da PDP ta sake tsayar da shi takara domin fafatawa a zaben shekarar 2023.