Sojoji sun yi wa ‘yan ta’addan da suke wucewa da makamai a yankin Birnin Gwari kwanton bauna

0 222

Dakarun sojojin da aka tura jihar Kaduna domin yaki da yan ta’addanci sun yi wa ‘yan ta’addan da suke wucewa da makamai a yankin Birnin Gwari kwanton bauna a jiya Laraba.

A cewar rundunar sojin  wannan harin kwanton bauna ya biyo bayana samun bayanan sirrin da suka samu.

Sojojin sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna a kewayen kauyen Kwaga, wadanda suka shahara wajen haddasa rikici a karamar hukumar Birnin Gwari, inda suka kashe wani dan ta’adda, yayin da wasu kuma suka gudu cikin.

Sunyi nasar kwato bindigu kirar AK 47 guda 2 da mujallu, da kuma babura 2.

Leave a Reply

%d bloggers like this: