An ci gaba da ƙidayar kuri’u bayan kammala zaɓen shugaban kasa a jiya a ƙasar Chadi

0 114

An kammala zaɓen shugaban kasa a jiya a ƙasar Chadi da nufin kawo karshen mulkin soji na tsawon shekaru uku.

Hukumar zaɓe ta ƙasar (Ange) ta ce an samar da tsauraran matakai na hana maguɗi yayin kidayar kuri’un.

Shugaban mulkin sojin kasar Janar Mahamat Idris Deby ya ce ya cika alkawuran da ya ɗauka wa ‘yan kasar Chadi na shirya zabe.

Babban abokin hamayyarsa Firaminista Succes Masra ya buƙaci ‘yan kasar Chadi da su fito da yawa don kaɗa ƙuri’arsu idan suna son “ganin wani gagarumin sauyi a kasarsu”.

Hukumar zaɓen zata sanar da sakamakon zaɓen nan da ranar 21 ga watan Mayu kuma idan babu ɗan takara da ya samu cikakkiyar rinjaye, za a gudanar da zagaye na biyu a ranar 22 ga watan Yuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: