An yi bikin rantsar da Vladimir Putin a matsayin shugaban Rasha karo na biyar
Nasararsa a zaɓen watan Maris na zuwa ne makonni da mutuwar fitaccen abokin hamayyarsa, Alexei Navalny, a gidan yari.
Wakilin BBC ya ce kusan shekaru 25 yanzu da Putin ke mulki a Rasha a matsayin shugaban ƙasa ko shugaban gwamnati
Ƙasashen yamma sun yi alla-wadai da zaɓensa a wannan lokaci da suka ce babu sahihanci da darajar dimokuraɗiyya.
Ƙasashen Amurka da na Tarayyar Turai sun ce za su ƙauracewa bikin da aka shirya a Kremlin.
kodayake Faransa da wasu ƙasashen na Turai za su tura wakilai duk da roƙon da Ukraine ta yi cewa su yi biris.