NLC ta bukaci CBN ya gaggauta janye sabon harajin da ya kaddamar kan harkar tsaro ta yanar gizo

0 99

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC, ta yi watsi da sabon harajin da babban bankin kasa CBN ya kaddamar kan harkar tsaro ta yanar gizo, inda ta bukaci a janye ta cikin gaggawa.

Shugaban kungiyar ta NLC, Comrade Joe Ajaero, a wata sanarwa da ya fitar, ya koka da cewa karin harajin wata manufa ce ta adawa da gwamnati a cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki.

Ya bayyana cewa harajin, wanda za a aiwatar ta hanyar cirewa daga farkon ciniki, wani nauyi ne da ke wuyan ’yan Najeriya masu aiki tukuru.

Ya kuma bayyana yadda Wannan matakin da nufin karfafa matakan tsaro ta yanar gizo, yana barazanar kara tabarbarewar kudin da jama’a ke fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: