EFCC na binciken wasu manyan jami’an tsaro 10 bisa zargin almundahanar kudi Naira Bilyan 7.5

0 108

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, na binciken wasu manyan jami’an hukumar tsaro da tsaron farin kaya ta kasa su 10, bisa zargin almundahanar kudi Naira Bilyan 7.5bn.

A cewar wata takarda da wakilin jaridar Punch ya samu na musamman, hukumar EFCC ta shirya yi wa jami’an da abin ya shafa tambayoyi daga ranar 2 ga watan Mayun 2024.

Zamban Naira Bilyan 7.5bn na da alaka da wasu ‘yan kwangila da kuma kudaden da aka samu daga wasu ma’aikatan ofishin canji wadanda ta hannun manyan jami’an suka yi awon gaba da kudaden.

Wata majiya ta ce, “Masu binciken EFCC sun gano cewa an biya jimillar ‘yan kwangila 20, yayin da aka ware Naira biliyan 2 ga manyan ‘yan kwangila guda uku wanda kowannensu ya mallaki kamfanoni biyar. 

Kowanne daga cikin ’yan kwangilar ya samu kudin rike da kashi 5%. 

Hukumar EFCC ta aike da wasikun gayyata ga ‘yan kwangilar.

A ci gaba da tabbatar da faruwar lamarin, wata majiya mai tushe ta bayyana cewa ‘yan kwangilar da ake tuhumar sun yi kalamai masu amfani da suka kai ga kwato kimanin Naira Bilyan 1 daga hannun hukumar EFCC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: