Karyewar gada ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 24 a lardin Guangdong na kudancin kasar China

0 101

Mutum 24 sun mutu a China bayan karyewar da gada ta yi a wata babbar hanya da ke lardin Guangdong na kudancin ƙasar.

Wani ɓangare ne na titin da ke kusa da wani tudu ne ya zaftare, lamarin da ya haifar da ɓallewar gadar.

Faifan bidiyo ya nuna tarin motoci da suka afka cikin katoton ramin da ya buɗe bayan zaftarewar wani ɓangare na titin.

Babu tabbas kan ko mamakon ruwan da aka tafka a cikin makwannin a yankin kudancin China ne ya raunanar da turakun babbar hanyar.

Yanzu haka dai an kai gwamman mutane asibiti inda suke samun kulawa sanadiyyar raunuka da suka samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: