Jirgi na biyu dauke da alhazan jihar Jigawa 553 ya sauka a filin jirgin sama dake Dutse

0 243

Jirgi na biyu dauke da alhazan jihar Jigawa 553 ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Nuhu Muhammad Sanusi dake Dutse babban Birnin jiha.

Jirgin na kamfanin Max air ya sauka ne da misalin karfe daya da minti daya na jiya alhamis.

Wakilinmu ya bamu labarin cewar alhazan sun sauka cikin lumana da kuma kwanciyar hankali

Haka kuma alhazan sun sami tarba daga yan uwa da kuma abokan arziki.

Alhazan da wakilinmu ya tattauna da su sun yi godiya ga Allah da ya basu wannan dama tare da godewa gwamnatin da hukumar alhazai ta jiha bisa dawainiyar da suka yi dasu anan gida da kuma kasa mai tsarki.

Ana sa ran kammala jigilar alhazan jihar Jigawa zuwa gida Nigeria a gobe asabar 12 ga wata.

Kawo yanzu an kawo alhazan jihar Jigawa 935 zuwa gida a sawu biyu na jiragen max air.

Leave a Reply

%d bloggers like this: