Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau ya tashi daga Abuja zuwa Malabo, babban birnin kasar Equatorial Guinea domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika na musamman wanda zai mayar da hankali akan tsaro. Shugaban kasar ya samu rakiyar mai dakinsa, Aisha Buhari, da Ministan Continue reading
A yau ne wanda yake 26 ga watan Mayun 2022 za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na ƴan takarar gwamnonin jam’iyyar APC mai ci. Hakazalika, ana kyautata zaton a yau ɗin ne za a gudanar da zaben fitar da gwani na ƴan majalisar wakilan tarayya. Anan jihar Jigawa yan takara mutum tara (9) […]Continue reading
Gwamnatin jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar yara 14 sakamakon barkewar cutar kyanda a kananan hukumomi tara na jihar. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Afam Obidike ne ya sanar da hakan a yau a wani taron manema labarai a Awka, babban birnin jihar. Ya ce a kalla mutane 414 ne suka kamu da cutar kyanda […]Continue reading
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun yi garkuwa da wani limamin Cocin Saint Patrick, Stephen Ojapa da mataimakinsa Oliver Okpara a kauyen Gidan Mai Kanbu da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina. Majiyoyin cikin gida sun bayyana cewa da sanyin safiyar yau ne ‘yan bindigar suka kai farmaki harabar […]Continue reading
Ofishin jakadancin kasar Sifaniya a Najeriya ya ce ya bayar da gudummawar allurai miliyan 4 da dubu 400 na rigakafin corona samfurin Johnson & Johnson ga gwamnatin tarayya don dakile yaduwar cutar ta corona. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a yau mai dauke da sa hannun ofishin jakadanci ya fitar a Abuja. […]Continue reading
Fadar shugaban kasa ta gargadi jama’a da su guji yada labaran karya a shafukan sada zumunta, don hana masu son raba kan kasar damar yin hakan. Har ila yau, fadar ta yi gargadi game da mayar da martani cikin fushi, da haifar da firgici, da tabarbarewar rayuwa da asarar rayuka, da ma tashe tashen hankula […]Continue reading
‘Yan haramtacciyar kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra, a ranar Lahadi sun kashe ‘yan Arewa 10, ciki har da mace mai juna biyu, da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a kauyen Isulo dake karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar Anambra. An bayyana sunan matar da aka kashe da Harira Jibril mai shekaru […]Continue reading
Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari a karshen mako. Shaidu sun ce ‘yan bindiga ne a kan babura suka yi wa mutanen garin luguden wuta a lokacin da suka shiga daji domin dibar itace. A cewar […]Continue reading
Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, a jiya ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023. Habu Zarma, wanda shi ne jami’i mai kula da zaben, ya ce Dankwambo ya samu tikitin ne biyo bayan janyewar sauran ‘yan takara biyu, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Usman Bayero […]Continue reading
A jiya ne aka zabi tsohon gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Saminu Turaki a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Jigawa ta arewa maso yamma. Saminu Turaki wanda ya koma jam’iyyar PDP kwanan nan ya ci zabe babu hamayya a zaben da ya gudana a karamar hukumar Gumel. Haka kuma, an zabi […]Continue reading