Home Archive by category Labarai (Page 2)

Labarai

Labarai

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bayyana goyon bayanta ga mata masu neman tsayawa takara a zaben 2023

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, jiya a Abuja, ta bayyana goyon bayanta ga mata masu neman tsayawa takara a zaben 2023. Aisha Buhari ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ziyarci Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa. Bayan ganawar sirri da Abdullahi Adamu, uwargidan Continue reading
Labarai

Rundunar hadin gwiwa ta kasa-da-kasa ta gano wata kasuwar kifi ta boye da mayakan Boko Haram dana ISWAP

Rundunar hadin gwiwa ta kasa-da-kasa ta gano wata kasuwar kifi ta boye da mayakan Boko Haram dana ISWAP suke mu’amala da ita dake yammacin Afirka a gabar tekun tafkin Chadi. Rundunar ta kara da cewa an kama mutane a kalla 30 wadanda  masunta ne da manoma a kasuwar. A cikin wata sanarwa da babban jami’in […]Continue reading
Labarai

Gwamna Badaru ne ya maida jihar Jigawa sabuwar duniya cikin shekaru shida – Ahmad Lawan

Shugaban majalissaar dattawa ta kasa Sanata Ahmed Lawan ya jinjinawa al’ummar jihar jigawa da gwamantin jiharnan murnar samun nasarorin gudanar da ayyukan cigaban jiha, da kuma kammala manyan ayyuka a fadin jihar nan. Lawan ya bayyana hakan ne a lokacin dayake ganawa da masu ruwa da tsaki da kuma deligates na jam’iyyar APC a birnin […]Continue reading
Labarai

Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarar majalissar dokokin jiha da na majalissar wakilai ta kasa

Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarar majalissar dokokin jiha da na majalissar wakilai ta kasa a fadin jihar. Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Jigawa Babandi Ibrahim Gumel ne ya bayyana hakan, a lokacin dayake zantawa da manema labarai. Ya kuma yabawa jagoran jam’iyyar PDP kuma tsohon gwamnan […]Continue reading
Labarai

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta karbi yan Najeriya 129 da suka makale a garin Agadez na jamhuriyar Nijar a Kano

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta karbi Yan Najeriya 129 da suka makale a garin Agadez na jamhuriyar Nijar a Kano. Kodinetan hukumar a ofishin reshen jihar Kano Nuradeen Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi mutanen da aka dawo da su. Kamfanin Dillancin Labaran na kasa NAN ya bayar […]Continue reading
Labarai

Ta tabbata Anamekwe Nwabuoku shine wanda gwamnatin tarayya ta nada a matsayin sabon Akanta Janar na rikon kwarya a madadin Ahmad Idris

Awani cigaban kuma Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Anamekwe Nwabuoku a matsayin sabon Akanta Janar na rikon kwarya na kasa. Babban sakataren ma’aikatar kudi kasafi da tsare tsare ta kasa Aliyu Ahmed ne tabbatar da nadin, cikin wata takarda mai dauke da kwannan watan 20 ga wata Mayu na 2022, mai dauke da sa […]Continue reading
Labarai

Babban bankin Kasa na CBN yace yan Najeriya sun kashe sama da naira biliyan 100 kan ilimi a ƙasashen waje cikin watanni uku

Wata ƙididdiga daga Babban Bankin Najeriya wato CBN ta nuna cewa ƴan Najeriya sun kashe aƙalla dala miliyan 220.86 kan karatu a ƙasar waje daga Disambar 2021 zuwa Fabrairun 2022. Hakan na nufin sun kashe sama da naira biliyan 100 a kuɗin Najeriya. Jaridar Punch a ƙasar ta ruwaito cewa CBN bai bayyana adadin da […]Continue reading
Labarai

Delegates din jihata Rotimi Amaechi zasu zaba a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani da ke tafe a cewar gwamnan jihar Plateau

Gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong, ya ce Delegates din Jam’iyar APC na Jihar zasu zabi Rotimi Amaechi, a matsayin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar a zaben fidda gwani da ke tafe. Da yake jawabi ga Amaechi da Delegates na Jam’iyar APC a gidan Gwamnati da ke Jos a jiya, Gwamna Lalong, ya ce Rotimi […]Continue reading
Labarai

Zan inganta fannin noma a jihar Jigawa matukar an zabe ni a matsayin shugaban kasa – Ibekunle Amosun

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun kuma dan takarar shugaban kasa a Jam’iyar APC Ibekunle Amosun, ya ce zai inganta fannin Noma a Jihar Jigawa matukar an zabe shi a matsayin shugaban kasa. Sanata Amosun, ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki da kuma Delegates na Jam’iyar APC ta Jihar Jigawa da ke Dutse […]Continue reading
Labarai

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya bukaci masu neman kujerar shugaban kasa su sanya bukatar Najeriya sama da tasu

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma Jigo a Jam’iyar PDP Sule Lamido, ya bukaci masu neman kujerar shugaban kasa su sanya bukatar kasa a sama da tasu fiye da komai. Sule Lamido, ya bayyana hakan ne a lokacin da yan takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyar PDP wanda suka hada da Anyim Pius Anyim, da Bukola Saraki […]Continue reading