Tinubu Ya Sabunta Wa’adin Injiniya Abdul’azeez A Matsayin Shugaban TCN

0 230

Shugaba Bola Tinubu ya sabunta naɗin Injiniya Sule Ahmed Abdul’aziz a matsayin shugaban kamfanin dakon wutar lantarki na ƙasar, TCN a wani sabon wa’adi na shekara huɗu wanda shi ne na ƙarshe.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce an sabunta naɗin Injiniya Abdul’aziz ɗin ne sakamakon ƙwazon da ya nuna a tsawon lokacin da ya kwashe yana jagorancin kamfanin a wa’adinsa na farko.

Sanarwar ta ƙara da cewa Injiniya Abdul’aziz ya samar da cigaba na a-zo-a-gani dangane da wutar lantarki inda ya yawaita wutar da zamanantar da tsarin da kuma tabbatar da tsarin dakon wuta a Najeriya.

Wannan sabunta naɗin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin wuta duk kuwa da yadda suke kokawa suna biya da tsada.

Leave a Reply